
Senator Shehu Sani, wanda tsohon Sanata ne, ya ƙalubalanci shirin kirkirar ‘yan sandan jiha don daƙile matsalar rashin tsaro kamar yadda shugaban kasa Bola Tinubu ya Yi umurni.
Shehun Sani ya bayyana hakan cewa wata hanya ce ta neman kada a zauna lafiya.
A wani taron gaggawa da suka yi a Abuja ranar Alhamis, Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin ƙasar nan sun tattauna yiwuwar kirkiro ‘yan sandan jihohi domin tunkarar wasu matsaloli musamman na tsaron da ke addabar al’umma.
Tsohon Sanatan ya nuna rashin amincewa da hakan, inda ya ce gwamnonin za su iya ɗaukar ‘yan daban jam’iyyar su aiki cikin ‘yan sandan jihar su yi amfani da su wajen muzgunawa ‘yan adawa.
Sani ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafin shi na X a ranar Litinin.
Sani ya ce, “Gwamnoni za su yi amfani da ‘yan sandan jihar wajen muzgunawa ‘yan adawa, da takurawa waɗanda ba ‘yan asalin jihar su ba, da yin maguɗin zaɓe da kuma tinkarar ‘yan sandan tarayya idan aka samu saɓani tsakanin gwamnatin tarayya da jihar. Mafi akasarin ‘yan daban jam’iyya mai mulki a jihar ne za a ɗauka aiki cikin ‘yan sandan jihar.”
Tsohon ɗan majalisar tarayyan ya ce babu wani sihiri da ‘yan sandan jiha za su yi da sojoji da ‘yan sandan tarayya da kuma jami’an tsaron farar hula ba su yi ba.
Ya ƙara da cewa, “tunanin cewa ‘yan sandan jiha za su magance duk matsalolin tsaro da ake fama da su a ƙasar nan, mafarki ne. Wane sihiri ne ‘yan sandan jiha za su iya yi wanda sojoji da ‘yan sanda da na farar hula ba za su iya ba? Rundunar ‘yan sandan jiha za ta zama reshen jam’iyya mai mulki na kowace jiha da ke ɗauke da makamai. Wata hanya ce ta rashin zaman lafiya.”
A makon da ya gabata ne Cibiyar Kula da Doka ta Ƙasa (RULAAC) ta goyi bayan shirin ‘yan sandan jihohi a cikin halin rashin tsaro da ake fama da shi a ƙasar.
RULAC ta ce gwamnonin jihohi sun bayar da kuɗi kashi mafi tsoka na ayyukan ‘yan sanda a tsawon shekaru.
Ta ce gwamnatin tarayya tana kallon hakan a matsayin gudunmawa kawai, don haka akwai buƙatar jihohi su kare yankunan su.