Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Daurawa, ya sasanta tsakaninsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ya koma kan muƙaminsa.
Duk da murabus ɗin da Daurawa ya yi a wani faifan bidiyo ta kafar sadarwar zamani, bai yi murabus bisa ƙa’ida a rubuce ba kuma ya miƙa wa hukumar da ta dace.
A wani sabon cigaba a daren Litinin, Daurawa ya gana da gwamnan tare da wasu manyan mutane.
Shugaban na Hisbah zai koma aiki ranar Talata, kamar yadda majiyar gwamnati ta bayyana.
Gwamnatin Jihar Kano ta daɗe tana ƙoƙarin mayar da Shehin Malamin da aka yi masa ba daidai ba.
An tattaro cewa an aike wata tawaga ta manyan malaman addinin Islama mai suna Zauren Haɗin Kan Malamai zuwa Daurawa domin su kwantar da hankalinsa ya koma kan muƙaminsa na shugaban Hisbah.
Wata majiya ta shaida cewa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Falgore, da Babban Limamin Masallacin Ƙasa na Abuja, Sheikh Ibrahim Maqari, suma gwamnati ta aike su domin ganawa da shi.
Gwamna Yusuf ya soki tsarin ‘operation kau da baɗala’ – wani shiri na hukumar Hisbah da nufin yaƙi da lalata a jihar.
Daurawa ya yi murabus ne ƙasa da sa’o’i 24 da sukar gwamnan kuma hakan ya jawo martani da kakkausar murya daga jama’a.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya damu kan lamarin, wanda yasa ganawar ta ranar Litinin.