A ranar Lahadi ne Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa Maiduguri domin gudanar da bukukuwan ƙaramar salla, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito.
A lokacin da Shettima ya isa filin jirgin saman Muhammadu Buhari na ƙasa da ƙasa da ke Maiduguri, ya samu tarba daga Mataimakin Gwamnan Borno, Alhaji Umar Kadafur, da ‘Yan Majalisar Zartarwa na Jiha da jiga-jigan jam’iyyar.
A halin da ake ciki dai an tsaurara matakan tsaro a Maiduguri da kewaye kamar yadda aka saba a lokutan bukukuwa irin wannan.
Ana sa ran gudanar da bikin ƙaramar sallah na ƙarshen azumin watan Ramadan ko dai Talata ko Laraba dangane da kalandar Wata da ke shelanta sabon watan Musulunci na Shawwal.