Back

Shirin ba da lamuni na ɗalibai zai sanya su cikin bashi na dindindin -ASUU

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta ce shirin bayar da lamuni na karatu zai sanya daliɓai cikin ha’ula’in bashi na dindindin.

A cewar wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar a ranar alhamis bayan taron ta na Majalisar Zartaswa ta Ƙasa (NEC) a jami’ar Neja Delta, Wilberforce Island, jihar Bayelsa, ASUU ta ce ta yi mamakin rahotannin da ta samu kan gazawar gwamnatin Bola Tinubu na magance matsalolin da suka dabaibaye su wanda ya tilastawa ƙungiyar tafiya yaji aikin a faɗin ƙasar daga watan biyu zuwa watan goma na shekara ta dubu biyu da ashirin da biyu.

Gwamnatoci da suka wuce a Najeriya a ko dayaushe sun yi watsi da yarjejeniyoyin da suka rattaba hannu da ƙungiyar wanda ya sanya ƙungiyar ta yi amfani da yajin aiki don ƙwato hakkin ta.

Sai dai abin takaicin shi ne, wasu daga cikin waɗannan yarjejeniyoyin da suka haɗa da biyan kuɗaɗen alawus, da kuma rashin ci gaba da tattaunawa a kan yarjejeniyar ASUU da Gwamnatin Tarayya na shekara ta dubu biyu da tara, da cire su daga Haɗin Tsarin Bayanan Biyan Albashin Ma’aikata (IPPIS), kuɗaɗen farfaɗo da jami’o’i, da albashin da gwamnatin Bata biya ba, suna daga cikin dalilan da yake kawo sabani tsakanin gwamnati da ASUU.

Amma ASUU ta dage kan cewa Tsarin Lamuni na Ɗalibai, da hukumomin bayar da lamuni na duniya suka tallata su kamar Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya zai hana jami’o’in gwamnati samun kuɗaɗe.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Don kauce wa shakku, Hukumar NEC ta ASUU ta sake nanata ƙin amincewa da Shirin Bayar da Lamuni na Ɗalibai wanda hukumomin bayar da lamuni na duniya irin su IMF da Bankin Duniya ke gabatarwa.

“Ya kamata ‘yan Najeriya su sani cewa wannan shiri wata hanya ce ta hani ga jami’o’in gwamnati samun kuɗaɗe da kuma dabarar karkatar da kuɗaɗen jama’a zuwa jami’o’i masu zaman kan su mallakar wasu ‘yan siyasa da abokan su.

“Majalisar Zartaswa ta Ƙasa, ta ci gaba da lura da cewa tsarin ba da lamuni na ɗaliban zai jinginar da dukkan jami’o’in tare da sanya daliban mu cikin basussuka na dindindin.

“Idan har shirin zai iya gazawa a wasu ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi, to babu tabbacin zai yi nasara a Najeriya inda cin hanci da rashawa, son kai, da sauran munanan abubuwa da suka haɗu wajen kashe aikin Bankin Ilimi bayan sama da shekaru biyar da kafa shi.”

Sai dai ASUU ta ba da shawarar cewa idan da gaske gwamnatocin jihohi da na Tarayya na son zuba jari a rayuwar daliɓan Najeriya, a ba wa ɗalibai tallafin kuɗaɗe da ɗaukar nauyin karatunsu kuma a maido da Tsarin Kasafin Kuɗi na Buƙatu zuwa tsarin jami’o’i domin samun inganci mafi girma.

Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, a cikin sanarwar, ya ce ƙungiyar ta yi Allah-wadai da ƙarin maƙudan kuɗaɗe a makarantu, inda ta ce a yi amfani da kuɗaɗen da aka karkatar daga baitul-malin gwamnati wajen ɗaukar nauyin jami’o’i.

Ya ce, “Majalisar Zartaswa ta Ƙasa gaba ɗaya ta yi Allah-wadai da ƙarin kuɗaɗen da ake yi ba tare da ta cewar waɗanda abin ya shafa ba a jami’o’in mu.

“Rahotanni na yau da kullum na badaƙalar maƙudan kuɗaɗe da aka karkatar daga asusun gwamnati a matakin jihohi da na tarayya na ƙarfafa imanin mu cewa albarkatun da ake samu a ƙasar za su iya tallafawa ilimin jami’o’i da gwamnati ke ɗaukar nauyi, ba tare da matsananciyar matsin lamba ga iyaye ba kamar yadda ake yi a halin yanzu.”

Ya yi bayanin cewa da Gwamnatin Tarayya ta cika alƙawarin yarjejeniyar da aka cimma a shekarar ta 2013, wadda ta tanadi Naira tiriliyan N1.3 na tsawon shekaru shida, da an maido da jami’o’i da dama zuwa matakin da za su iya jawo hankalin ɗalibai daga ƙasashen waje da kuma yin suna wajen yin bincike da zai kawo cigaba da canji.

Muna ƙalubalantar gwamnatin Tinubu da ta gaggauta fara wani yunƙuri don gudanar da wani aikin tantance buƙatu don tabbatar da haƙiƙanin kiran da muka yi na shiga tsakani a jami’o’inmu.

“Martanin Gwamnatin Tarayya kan ƙalubale makamancin haka a shekarar 2012 ne ya haifar da jimillar Naira Tiriliyan 1.3 da Gwamnatin ta soke tun daga lokacin,” in ji ta.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?