
Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa Super Eagles bisa ƙwazon da suka nuna a Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) na Hukumar Ƙwallon Ƙafar Afirka (CAF) na shekarar 2023 da aka kammala a Cote d’Ivoire.
Najeriya ta gaza ɗaukar kofin gasar, bayan da ta sha kashi a hannun ƙasar Cote d’Ivoire da ci 1-2 a filin wasa na Alassane Ouattara da ke Abidjan, a daren Lahadi.
Sai dai kuma a wata sanarwa da Mai ba shi Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar, Shugaba Tinubu ya ƙarfafa wa ‘yan Najeriya gwiwa da su yi farin ciki duk da rashin nasarar da aka samu, inda ya yi nuni da cewa ƙwazon Eagles da jajircewar da suka yi a duk lokacin gasar ya samu soyayyar ƙasashen Afirka da ma duniya baki ɗaya.
“Shugaba Bola Tinubu ya jinjinawa Super Eagles na Najeriya bisa jajircewar da suka nuna a wasan ƙarshe na Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) na 2024 a Cote d’Ivoire.
“Shugaba Tinubu ya yabawa ‘yan wasan, mai horaswan, ma’aikata, da ɗaukacin tawagar gudanarwa bisa ƙwazonsu, da sadaukarwar da suka yi a gasar, tare da amincewa da matsalolin da suka ci gaba da wucewa da inganta ayyukansu yayin da suke ci gaba da samun nasara zuwa wasan ƙarshe.
“Shugaban ya buƙaci ‘yan Najeriya da su yi farin ciki, yana mai jaddada cewa mun samu gagarumar nasara a zukatan Afirka da ma duniya baki ɗaya ta hanyar dagewa da jajircewa a fagen wasa”, in ji sanarwar.
Shugaban, a cewar sanarwar, ya buƙaci ‘yan Najeriya da kada su bari wannan rashi ya karya musu gwuiwa, amma su bar abunda ya faru ya haɗa kansu domin su ƙara himma, tare da ƙarfafa wa matasa ‘yan ƙasa gwiwa, masu burin kawo ɗaukaka ga ƙasar nan ta hanyar wasan ƙwallon ƙafa cewa kada su yi ƙasa a gwiwa, kamar yadda gwamnatinsa take aiki don ganin burikansu sun tabbata.
“Kada wannan abin da ya faru ya karya mana gwuiwa, amma ya haɗa mu don yin aiki tuƙuru. Mu al’umma ce mai girma, an ɗaure mu ɗaya da tutar kore-fari-kore na juriya, farin ciki, bege, aiki, da ƙauna marar gajiyawa.
“Ga matasan Najeriya masu ƙima da suke nuna baiwan su a cikin al’umma, suna yin layi a cikin yashi yayin da suke buga wasan ƙwallon ƙafa a cikin ƙasƙantattun filayen su na wasan ƙwallon ƙafa, za ku iya zama jarumanmu gobe, kada ku yi ƙasa a gwuiwa wajen neman ku. Gwamnatina tana nan don tabbatar da burikanku,” in ji Shugaban.