A ranar Litinin, ashirin da shida ga watan Fabrairu ne Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ƙaddamar da wasu hanyoyi guda uku da gwamnan jihar Abia, Alex Chioma Otti ya gyara.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar, Prince Okey Kanu ya sanya wa hannu, wanda aka rabawa manema labarai a safiyar ranar Asabar.
Wannan dai shi ne karo na farko da Shugaban Ƙasar zai ƙaddamar da wata hanya da gwamnonin da ke kan mulki a yanzu a Najeriya suka gina.
Wani ɓangare na sanarwar da gwamnatin Abia ta fitar na cewa: “Hanyoyin da za a ƙaddamar su ne; titin Omoba, titin Jubilee da titin Queens a jihar Abia.
“Hakazalika wannan ita ce hanya ta tara da aka ƙaddamar a Abia tun bayan da Dr Alex Otti, OFR, ya karɓi ragamar mulkin jihar watanni takwas da suka gabata.
“Shugaban Ƙasan zai kuma ƙaddamar da tashar samar da wutar lantarki a Abia a ranar Litinin, ashirin ga watan Fabrairu; tashar wutar lantarki da za ta samar da wutar lantarki ba tare da katsewa ba ga Abia da kewaye.