
Shugaban Ƙasar Iran, Ebrahim Raisi
Shugaban Ƙasar Iran, Ebrahim Raisi, ya mutu bayan wani jirgin sama mai saukar ungulu ɗauke da shi da wasu jami’ai ya yi hatsari.
An ruwaito cewa mutane 9 na cikin jirgin a lokacin da jirgin ya faɗo a Arewacin lardin Azarbaijan na Iran da ke Gabashin Ƙasar kuma ana kyautata zaton dukkansu sun mutu.
Rahotannin sun zo ne bayan da masu ceto daga ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta Iran suka ce sun gano tarkacen jirgin mai saukar ungulu, wanda kuma ke ɗauke da Ministan Harkokin Wajen Ƙasar da wasu jami’ai, kuma “babu alamar wani mai rai.”
Tawagar masu aikin ceto sun yi artabu ta hazo da guguwa da tsaunuka don isa ga tarkacen jirgin a yankin Gabashin Azarbaijan da sanyin safiyar Litinin ɗin nan, sai dai gidan talabijin na gwamnatin ƙasar bai bayar da cikakken bayanin musabbabin hatsarin ba.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya habarta cewa, tare da Raisi akwai Ministan Harkokin Wajen Ƙasar, Iran Hossein Amirabdollahian, Gwamnan Lardin Gabashin Azarbaijan da sauran jami’ai da masu gadi.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, “jirgin saman Shugaban Ƙasar Raisi ya ƙone gaba ɗaya a cikin hatsarin…ana fargabar duk fasinjojin sun mutu.”