Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA), Yakubu Maikyau, ya koka kan rawar da wasu lauyoyi da kotuna suka taka wajen yanke hukunce-hukunce masu cin karo da juna dangane da rikicin masarautar Kano, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin kunya ga aikin shari’a.
Wasu kotuna biyu a Jihar Kano sun bayar da wasu umarnin wucin gadi masu cin karo da juna kan rikicin masarautar Kano.
Mai Shari’a S. A. Amobeda na Babbar Kotun Tarayya da ke Kano a ranar Talata ya bayar da umarnin korar mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II daga Fadar Gidan Rumfa.
Sai dai Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu na Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da wani umarni na daban, inda ta haramtawa ‘yan sanda da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS) da kuma rundunar sojojin Nijeriya daga kora, muzgunawa ko kama Sanusi.
Sarki Sanusi da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, sun fafata da juna domin neman kujerar sarauta.
Rikicin dai ya janyo zanga-zangar magoya bayansu a Kano.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Maikyau, Babban Lauyan Nijeriya (SAN) a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda lauyoyi da alƙalan da ke da hannu a cikin shari’ar suke gudanar da ayyukansu.
Ya yi nuni da cewa akwai buƙatar a sake yin nazari cikin gaggawa kan yadda ƙwararrun lauyoyi da kuma alƙalan da ke da ruwa da tsaki a waɗannan al’amura ke gudanar da ayyukansu.
Shugaban NBA ya yi kira ga shugabannin kotunan da su binciki yadda alƙalan ke gudanar da ayyukansu tare da kai rahoton bincikensu ga Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta ƙasa (NJC) domin ɗaukar matakin da ya dace.