
HERBERT Wigwe, tsohon Manajan Darakta na Bankin Access kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Access Holdings, ana zaton ya rasu.
An ruwaito cewa Wigwe yana cikin wani makeken jirgi mai saukar ungulu ne tare da matar sa, dan sa da wasu fasinjoji uku lokacin da abin takaicin ya faru a garin California, ta kasar Amurka
An ba da rahoton cewa suna kan hanyarsu ne ta zuwa garin Las Vegas domin su kalli kwallon Super Bowl, wasan zakaru na shekara-shekara na Hukumar Kwallon Kafa ta Ƙasa (NFL) ta Amurka.
Jaridar New York Times ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta boye sunayen fasinjojin.
Sai dai wasu majiyoyi daga masana’antar bankin sun tabbatar cewa shugaban bankin na cikin jirgin.
Za a samu cikakken bayani nan ba da jimawa ba….