Back

Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Kaduna ya ɗora wa jami’an Kaduna aikin jin daɗin alhazai

Malam Salihu S. Abubakar

Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, Malam Salihu S. Abubakar, ya ce an zaɓo jami’an aikin Hajjin 2024 ne bisa cancanta, don haka ya kamata su yi wa alhazai hidima gwargwadon iyawarsu da tsoron Allah.

Shugaban ya yabawa Gwamna Uba Sani bisa baiwa hukumar damar zaɓar ƙwararru kuma gogaggun mutane da zasu sauƙaƙa aikin hajjin bana a ƙasar Saudiyya.

Ya kuma gargaɗi jami’an da kada su sassauta ayyukan da za su yi na alhazai.

Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Alhazan, Yunusa Mohammed Abdullahi, ya fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa shugaban hukumar ya yi wannan gargaɗin ne a yayin taron farko tsakanin jami’ai da mambobin kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin tabbatar da gudanar da aikin hajjin bana cikin sauƙi, da kuma gudanarwar hukumar.

Mata maniyyata a wurin taron

Malam Salihu ya gargaɗi jami’ai kan karɓar cin hanci kafin ko bayan taimakon alhazai domin hakan haramun ne a Musulunci.

Ya ce: ‘’Mu nemi ladanmu a wurin Allah (SWT). Mu yi iya ƙoƙarinmu wajen gamsar da mahajjata, mu riƙa sauraron kokensu a duk lokacin da suka taso.

“Tun da farko mun gargaɗi dukkan jami’an rajista da na alhazai kan duk wani nau’i na karɓar kuɗi daga maniyyata. Don haka ya kamata jami’ai su daina karɓar kuɗi kafin su yi hidima.”

Malam Salihu ya kuma gargaɗi jami’an rajistar maniyyata kan karɓar kuɗin Hadaya domin yanka rago a lokacin aikin Hajji.

Ya nanata cewa a baiwa maniyyatan da ke da niyyar yin ajiya a banki telan banki domin yin ajiya a naira, daidai da yadda ake yin canjin dala.

A cewarsa, duk wani ƙorafi da aka yi akan wani jami’i, za a yi bincike sosai kuma idan aka same shi da laifi, za a miƙa shi ga hukumomin tsaro domin gurfanar da shi a gaban kuliya.

Ya kuma roƙi jami’ai da su yi aiki tuƙuru domin samun nasarar aikin Hajjin bana, ba tare da la’akari da kuɗi ko wata lada da za su samu daga aikin hajjin ba.

Ya shawarci jami’an da za su yi aikin Hajji na farko da su yi koyi da waɗanda suka je aikin Hajji a baya, domin yi wa alhazan Jihar Kaduna hidima gwargwadon iyawarsu da kuma tsoron Allah SWT.

Malam Salihu ya ce shi da mambobin hukumar da kuma mahukuntan hukumarsa sun duƙufa wajen gudanar da aikin Hajji cikin nasara, don haka ya kamata jami’ai su taimaka musu wajen samun nasara.

Shugaban ya ƙara da cewa a ayyukan da hukumar ta yi a baya ta samu labarin cewa wasu jami’ai sun yi watsi da alhazai a ƙasa mai tsarki tare da ci gaba da gudanar da ayyukan hajjin nasu, inda ya yi gargaɗin cewa ba za a amince da hakan ba a lokacin aikin hajjin bana.

Malam Salihu ya ce za a raba jami’ai zuwa kwamitoci ne bisa la’akari da cancantar su.

Ya tunatar da jami’an cewa duk wanda yake ganin ba zai iya bada gudummawa a kwamitin da aka naɗa shi ba to ya faɗi inda ya fi so.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?