Back

Shugaban kasa Tinubu ya sa kan dokar samar da wutar lantarki, da aka yi wa gyaran fuska

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu akan kudirin dokar samar da wutar lantarki (wadda aka yi wa gyara) ta shekarar 2024. Mataimaki na musamman ga shugaban kasar akan harkokin jarida, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a yau jumma’a.

Majalisar Wakilai ta amince da kudurin a ranar ashirin da bakwai ga watan bakwai na shekarar da ta gabata, dokar ta kuma samu amincewar Majalisar Dattawa a ranar sha hudu ga watan sha daya na shekarar da ta wuce wadda Honorabul Babajimi Benson, mai wakiltar mazabar tarayya ta Ikorodu ta jihar Legas ya dauki nauyi.

Kudirin dokar samar da wutar lantarkin ta wannan shekarar, na neman magance ci gaba da matsalolin muhalli na al’ummomin da suka karbi bakuncin kamfanonin dake samar da wutar lantarkin, da kuma ware kashi biyar cikin dari na ainihin kudaden gudanar da ayyukan kamfanonin da ke samar da wutar lantarkin (GENCOs) na shekara-shekara daga shekarar da ta gabata domin bunkasar nasu al’ummar masu masaukin baki.

Kudirin ya ci gaba da cewa, kudaden da aka ware domin ci gaban al’ummomin da za su karbi bakuncin kamfanonin, za a karbo, a sarrafa su, da kuma gudanar da su domin samar da ababen more rayuwa a cikin al’ummomin da suka karbi bakuncin ta hannun wani amintaccen mai rikon amana ko Manaja wanda GENCO da al’ummar da suka karbi bakuncin su za su nada tare.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?