Back

Shugabannin jam’iyyar APC na jihohi 37 sun goyi bayan Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa

Abdullahi Umar Ganduje

Shugabanin jam’iyyar APC mai mulki na jihohi 37 a ranar Talata, sun kai ziyarar nuna goyon baya ga Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, inda suka bayyana cikakken goyon bayansu ga Ganduje.

Ziyarar na zuwa ne bayan wata ƙungiya a Jihar Kano ta dakatar da shugaban na ƙasa.

Da yake jawabi yayin ziyarar, ƙungiyar, ƙarƙashin jagorancin muƙaddashin shugabanta kuma shugaban jam’iyyar na Jihar Legas, Cornelius Ojelabi, a sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa, ya bayyana waɗanda suka yi iƙirarin dakatar da Ganduje a matsayin ‘yan yaudara da ba su da wata manufa mai kyau ga jam’iyyar.

“Mun zo nan ne don mu sanar da kai cewa kai ne kyaftin na jirgin. A tare da ni kuma akwai magoya bayan ka a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya,” inji shi.

“Mun zo nan ne domin mu nuna haɗin kan mu da kuma jajircewar mu don godewa abin da NWC ke yi wa jam’iyyar. Za mu ba ku cikakken goyon bayanmu.

“Ka fara tafiya kan sake fasali da kuma faɗaɗa jam’iyyarmu. Muna da tabbacin kana kan hanya. Daga abin da muke gani, waɗanda suka ƙulla maƙarƙashiyar ma ba ‘yan jam’iyyarmu ba ne. Don haka ba za a bar su su kawo wa jam’iyyar mu cikas ba.”

Da yake mayar da martani, Ganduje, wanda ya zargi gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin Gwamna Abba Yusuf da shirya maƙarƙashiyar tsige shi, ya ce bai kamata a kalli lamarin a matsayin abin mamaki ba idan aka yi la’akari da yadda jam’iyyar APC ta mamaye ƙasar nan.

Ya ce: “Gwamnatin Jihar Kano ce ta ɗauki nauyin wannan wasan kwaikwayo. Wannan wani nau’i ne na wasan kwaikwayo da muke kira Afirka magic, wanda ba zai kai dimokuraɗiyya ko’ina ba. Wannan wani sabon lamari ne da ba a taɓa ganin irinsa ba, inda ’yan wata jam’iyyar siyasa daban, ba ma zaɓaɓɓun ‘yan kwamitin gudanarwa ba, suke nuna kansu a matsayin ’yan jam’iyyar APC tare da ɗaukar matakan da ka iya shafar al’ummar ƙasar nan. Ba za a yarda da wannan ba.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?