Back

Shugabannin Kasuwanni A Kano Sun Yabawa Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Saboda Samar Da Tsaro 

Shugaban kasuwar Sabon Gari a Kano ya yaba da kokarin kwamishinan ‘yan sandan jihar Muhammad Hussaini Gumel.

Manajan Daraktan Kasuwar Abubakar Rimi, Malam Abdul Bashir Hussaini, Shugaban Kasuwar Singa, Kasuwar Galadima da wata Kungiya mai zaman kanta ta Kano Alternative for Poverty Eradication, sun mika godiyar su ga Kwamishinan ‘yan Sandan Jihar Muhammad Hussaini Gumel, bisa ga irin gagarumar gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban matasa da inganta zaman lafiya a jihar Kano.

“Kuna iya bakin kokarin ku wajen aikin ‘Yan Sanda a Kano kuma kasuwannin mu su samu tsaro a yanzu.” Kasuwar MD Abubakar Rimi ga CP Gumel.

Babban Manajin Darakta na Kasuwar Muhammed Abubakar Rimi, Kasuwar Singa da Galadima, sun bayyana cewa, aikin da CP Gumel yake yi sun tabbatar da cewa shi ne mutumin da ya dace da aikin maido da zaman lafiya a fadin jihar Kano. “Muna samun cikakken goyon baya da hadin kai daga ‘yan sanda a jihar. Lallai kana iya bakin kokarin ka wajen aikin ‘yan Sanda a Jihar Kano, saboda haka yanzu Kasuwannin mu sun kasance cikin kwanciyar hankali da tsaro.”

MD ya ci gaba da cewa, “bisa la’akari da dukkan ayyukan alheri da kuke yi, za mu ci gaba da ba ku dukkan goyon baya da hadin kai.”

A nasa jawabin kwamishinan ‘yan sandan, Mihammad Usaini Gumel, ya bayyana cewa, “Bayan na zama kwamishinan ‘yan sanda a kano, muna gudanar da ayyuka a karkashin wasu muhimman ginshikai guda uku wadanda suka hada da, bude kofa domin kowa ya kawo korafin shi, aiki da kwarewa da kuma rashin cin hanci da rashawa.”

“Rundunar ‘yan sandan da ke karkashi na za ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da tsaro ga kowane mazaunin jihar.

Ya kara da cewa, “ya kamata jama’a su lura cewa kofar mu a bude take a koda yaushe, ya kamata Kuma su dauki wannan ofishin a matsayin wani kari na ofishin ‘yan kasa.”

An kammala taron tare da gabatar da Mujallar Rundunar ‘yan sanda ta CP ga MD.

Hakazalika wata kungiya mai zaman kanta ta Kano mai suna Alternative for Poverty Eradication tana jinjinawa kwamishinan ‘yan sanda bisa kokarin shi na ganin jihar Kano ta kasance cikin koshin lafiya.

A nasa jawabin a madadin kwamishinan ‘yan sanda, DPO na yankin Bompai reshen Kano, SP Abdulrahman Mohammed Kanoma ya yabawa kungiyar bisa yadda ta nuna goyin bayan ta ga wanda ya samu nasarori wajen tserewa da kuma zama abin koyi ga al’umma.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?