Rundunar sojojin ruwan Najeriya, na Ibaka, a Akwa Ibom, ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi, tare da damƙe kwale-kwalen da suke ciki na katako da ke ɗauke da litar man fetur dubu biyar da ɗari daya.
Babban Kwamandan Rundunar, Kaftin Uche Aneke, ya miƙa waɗanda ake zargin, jirgin ruwan da kuma man fetur ɗin ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) da ke Ibaka a ranar Lahadi.
Aneke ya ce, tawagar ‘yan sintiri ta rundunar sojin ruwa ta cafke waɗanda ake zargin ne a ranar ashirin da biyu ga watan Fabrairu bayan wani rahoton sirri da aka samu game da ayyukan fasa ƙwauri a yankin.
“An tura jiragen sintiri na sojin ruwa domin katse hanzarin kwale-kwalen na katako.
“A cikin kwale-kwalen akwai ‘yan fasa ƙwaurin guda biyu da ake zargi sun dauko lita dubu biyar da ɗari daya na man fetur da aka ɓoye a ƙarƙashin buhunan doya, kwalayen abubuwan sha, sauran abubuwan sha, da kwalayen tayel na ƙasa da dama.” inji shi.
Aneke ya gargaɗi ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyin da ke yin haramtacciyar sana’ar da su daina ko su shirya fuskantar fushin doka.
Ya kuma gargaɗi masu aikata laifuka da su kaucewa gaɓar ruwan Najeriya, yana mai jaddada cewa hukumomin tsaro ba za su lamunci ta’addanci a yankunan gaɓar tekun ƙasar ba.
Shugaban sashin yaƙi da ɓarna na NSCDC a Akwa Ibom, Micheal Asibor, wanda aka damka wa waɗanda ake zargin tare da kayayyakin ya ba da tabbacin gurfanar da su a gaba kuliya.