Dakarun Samar da Tsaro na (OPSH), ta rundunar soji ta musamman dake wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato da wasu sassan jihohin Bauchi da Kaduna, sun yi watsi da cin hancin Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar daga wasu da ake zargin ɓarayin shanu ne a jihar.
Jami’in Yaɗa Labarai na rundunar, Kyaftin James Oya, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Jos.
Oya ya ce sojojin da ke aiki da Sashin Huɗu sun kuma kama mutunen biyu da ake zargin ɓarayin ne da suka ba su cin hanci.
Ya bayyana cewa ba kawai yabon jami’an takwas da suka ƙi karɓar cin hancin aka yi ba, amma kwamandan rundunar, Manjo Janar Abdusalam Abubakar ya musu sakayya.
“OPSH ta yi wa jami’anta takwas sakayya bisa ƙin karɓar cin hancin Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar daga wasu da ake zargin ɓarayin shanu ne a Filato.
“Jami’an takwas da aka tura a Sashin Huɗu na OPSH, sun kama shanu talatin da aka sace a wani gurin bincike da ke kusa da Bisichi a ƙaramar hukumar Barkin Ladi a jihar.
“An yi awon gaba da shanun na wani Shehu Umar ne a garin Mangu inda aka kai su wani wuri da ba a sani ba, yayin da dakarun mu suka kama su a lokacin da suke aikin bincike.
“Waɗanda ake zargin, Anas Usman mai shekaru ashirin da Gyang Cholly mai shekaru arba’in da biyu, nan take suka tunkari rundunar da nufin ba su cin hanci don su samu hanyar wucewa da shanun da aka sace.
“An ƙi amincewa da cin hancin kuma an kama waɗanda ake zargin da kuma kuɗaɗen da aka bayar na cin hancin,” in ji shi.
Oya ya ce kwamandan wanda ya yabawa sojojin bisa jarumtaka da kuma abin koyi, ya buƙaci sauran jami’an tsaro da su yi koyi da wannan katafaren mataki na kare rayuka da dukiyoyi a jihar.