
A ranar Larabar da ta gabata ne dakarun sojin Najeriya suka yi nasarar kubutar da wasu mata goma Sha takwas da aka yi garkuwa da su daga hannun ‘yan bindiga tare da mika su ga gwamnatin jihar Katsina.
Wannan nasarar ta samu ne bayan kwanakin baya da aka dauke wasu mutane hamdin da biyar ”yan rakiyar amarya da ake zargin ’yan fashi ne suka yi awon gaba da su a kusa da garin Damari da ke karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsinan.
Kwamandan runfuna ta 17, ta Rundunar Sojan Najeriya a Katsina, Birgediya-Janar Oluremi Fadairo, ya ce Matan sun kubuta ne a yayin da sojojin suka kai wani samame na ceto zuwa sansanin ’yan bindigar da ke dajin Yan-Tumaki da Dan-Ali.
Ya bayyana cewa sojojin sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan a cikin wata fafatawa da sojin suka yi da ‘yan ta’addan, inda suka yi nasarar kubutar da wadanda harin ya rutsa da su.
Daga nan Fadairo ya mika matan da abin ya shafa ga kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Dr. Nasiru Mu’azu.
Kwamandan ya bukaci jami’an da ke karkashin Birgrd din da su ci gaba da gudanar da irin wannan aikin ceto domin ganin an kubutar da sauran wadanda aka yi garkuwa da su.