Back

Sojoji sun ceto waɗanda aka yi garkuwa da su a Zamfara

Dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation Hadarin Daji (OPHD) sun daƙile wani yunƙurin yin garkuwa da mutane 10 a garin Tsafe da ke jihar Zamfara.

A cewar jami’in Yaɗa Labarai na Rundunar, Laftanar Suleiman Omale, a wata sanarwa da ya fitar a Gusau a ranar Laraba, sojojin sun amsa kiran da aka yi musu na neman ɗauki, inda suka yi nasarar fatattakar masu garkuwa da mutanen.

“Da suke amsa kiran gaggawa da aka yi a daren ranar 12 ga Maris, 2024, sojojin OPHD sun yi artabu da ‘yan bindigar a lokacin da suka isa garin Tsafe.

“Ta hanyar tsatsauran dabaru da jajircewa, sojojin sun yi galaba a kan ‘yan bindigar inda suka tilasta musu gudu da raunukan harbin bindiga ta cikin wani daji mai duwatsu, inda suka yi watsi da waɗanda aka sace.”

Omale ya ƙara da cewa, “A yayin sintiri da aka yi a yankin, sojojin da suka ƙware sun kama su tare da samun nasarar kuɓutar da dukkan mutanen 10 da aka yi yunƙurin sacewa tare da sada su da iyalansu.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?