Back

Sojoji Sun Damke Shahararriyar Mai Garkuwa Da Mutane A Lokacin Da Take Kokarin Karbar Kudin Fansa

Sojoji Sun Kame Shahararriyar Mai Garkuwa Da Mutane A Lokacin Da Take kokarin karbar kudin fansa a Jihar Taraba Najeriya. 

Bataliya ta 93 ta sojojin Najeriya sun kama wadda ake zargin wata mata ce da ta shahara wajen yin garkuwa da mutane a lokacin da take kokarin karbar kudin fansar wata mata da aka sace a Jihar Taraba.

Kakakin rundunar ya kuma bayyana cewa matar da ake zargi da yin garkuwa da mutanen mai suna Janet Igohia, ‘yar shekaru 31 an kamata ne bayan ta karbi kudi naira miliyan 1.5, domin biyan kudin fansa ga wani mutum da aka sace a yankin Chanchangi da ke karamar hukumar Takum ta jihar.

Igohia, ta bayyana cewa, a baya taba auren Voryor Gata wani fitaccen mai laifi kuma tsohon shugaba na biyu ga marigayi Gana Terwase, a halin yanzu Kuma tana auren shugaban kungiyar masu tsatsauran ra’ayi a kudancin Taraba. 

A cewarta, a baya ta auri wasu manyan masu aikata laifuka irin su marigayi Terkibi Gemaga wanda aka fi sani da Mopol, wanda shahararren mai garkuwa da mutane ne da sojoji suka kashe shekaru biyar da suka gabata.

An gano cewa matar da ake zargin ta taba auren wani fitaccen mai laifi wanda shi ne shugaba na biyu ga marigayiya Hana Terwase.

“Ta bayyana cewa ta auri marigayi Gana Terwase, da aka kashe a wani samame na hadin gwiwa na musamman shekaru uku da suka wuce,” inji shi.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?