A wani samame na baya-bayan nan da sojojin Nijeriya suka kai tare da haɗin gwiwar ‘yan banga sun yi nasarar kawar da wani ɗan ta’adda mai hatsarin gaske, wanda ke ɓadda kama a matsayin ɗan sanda a Sakkwato don aikata munanan laifuka.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Maj-Gen. Onyema Nwachukwu, ya ce ɗan ta’addan da aka kawar da shi a ranar Laraba 20 ga Maris 2024 ya sha yin amfani da kame-kame don yaudara da sace waɗanda basu zarge shi ba.
“An gudanar da wannan aika-aikar ne biyo bayan sahihan bayanan sirri kuma an kashe wanda ake zargin a wata arangama da suka yi da sojojin.
“Sojojin sun kuma bankaɗo tare da lalata wani gida da ‘yan ta’addan ke amfani da shi a matsayin wurin ɓoye ƙwayoyi da kuma ba da magani ga masu tada ƙayar baya,” inji shi.
Nwachukwu ya ƙara da cewa, “A wani samame na daban da suka kai a jihar Taraba, sojoji sun kashe wani ɗan ta’adda a ƙauyen Kutoko da ke ƙaramar hukumar Takum a jihar Taraba. Harin ya yi sanadin ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da ƙunshin harsashin bindiga mai ɗauke da zagaye 4 na harsashi 7.62mm.
“Waɗannan ayyuka sun nuna irin jajircewar sojojin Nijeriya wajen yaƙar ta’addanci da tada ƙayar baya, a ƙoƙarin tabbatar da tsaron ƙasa.
“Muna kira ga jama’a da su ci gaba da tallafawa sojojin, yayin da muke yaƙi da abokan gaba na ƙasar.”