Back

Sojoji sun Kashe ISWAP hudu, sun ceto Fasinjoji da aka yi garkuwa da su a Yobe

Dakarun rundunar sojojin Najeriya mai suna “Operation Hadin Kai” da ke sashe na biyu sun kashe ‘yan ta’addar kungiyar IS da ke yammacin Afirka guda hudu tare da kubutar da fasinjojin da aka yi garkuwa da su a Buni Yadi, jihar Yobe.

A cikin wata sanarwa da wani mai sharhi kan yaki da tada kayar baya da tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ya fitar jiya, ya ce arangamar ta faru ne a kauyen Lamisuri da ke cikin karamar hukumar Gujba, bisa wasu majiyoyin sirri da aka tabbatar.

Ya ce a ranar Juma’ar da ta gabata da misalin karfe goma na safe wasu ‘yan ta’adda dauke da makamai da suka zo akan babur mai kafa uku da masu kafa biyu suka tare wasu motoci da ke jigilar fasinjoji a kan hanyar zuwa Kwalejin Koyon Aikin Gona ta Jihar Yobe da ke kusa da Buni Yadi.

Ya ce a cikin gaggawar mayar da martani, an tura tawagar sojoji da ke sintiri domin fatattakar ‘yan ta’addar, biyo bayan gano wata hanyar tserewa da ‘yan ta’addan suka yi niyyar bi wadda kuma sojojin suka gano ta hanyar leken asiri.

Tawagar ta yi nasarar gano wata motar da aka yi garkuwa da ita, koriyar Volkswagen Golf mai lamba BBU 353 HD, dauke da mata da kananan yara biyu da aka ‘yan I SWAP din suka gudu suka bari a baya saboda kwazon da sojoji suka yi.

Bayan tabbatar da tsaron lafiyar fasinjojin tare da tabbatar da motar, tawagar sojojin da ke sintiri ta ci gaba da aikin ta na zakulo sauran ‘yan ta’addan tare da kwato sauran motoci da fasinjojin da aka sace.

Dagewar da sojojin suka yi, ya kai su kauyen Lamisuri, inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan.

 A yayin farmakin, an kawar da ‘yan ta’adda hudu, sannan an kwato babur mai kafa uku dauke da kayan abinci da aka sace. Wasu daga cikin maharan sun yi nasarar tserewa da raunukan da suka samu daga musayar wuta.

Ya ce sauran motocin biyu da aka sace ba a gansu a wurin ba, shaidu sun nuna cewa sun nufi unguwar Meleri da ke kusa da kauyen Goniri.

Tawagar sojojin ta bi hanyar zuwa kauyen Meleri, inda bayanai masu inganci suka nuna cewa daya motar ta nufi Buni Yadi, yayin da daya kuma aka hange ta hanyar zuwa Damaturu ta kauyen Katarko.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?