Back

Sojoji sun kashe shahararren shugaban ‘yan ta’adda da wasu ɓata-gari a Katsina

Sojojin Nijeriya sun yi nasarar kashe wani fitaccen shugaban ‘yan ta’adda mai suna Maiƙusa, wanda shi ne mataimakin shugaban ‘yan ta’addan da aka fi sani da Modi-Modi a Katsina.

Wannan bayanin yana ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar a ranar Talata a Abuja.

Nwachukwu ya ce sojojin sun bindige Maiƙusa da wasu ‘yan ta’adda uku a ranar Litinin, yayin wata arangama da suka yi a ƙananan hukumomin Kurfi da Safana na jihar.

Ya ce wannan aikin ya kuma yi nasarar kawar da ‘yan ta’adda a yankunan.

A cewar sa, sojojin sun fuskanci turjiya daga ‘yan ta’addan, amma suka yi galaba a kan su da ƙarfin harbi, inda suka kashe wasu yayin da wasu suka gudu cikin ruɗani.

A halin da ake ciki, Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya ce jami’an soji a cikin ‘yan watannin da suka gabata sun kashe aƙalla jagororin ‘yan ta’adda bakwai a ƙasar nan.

Ministan ya bayyana haka ne a wata hira da manema labarai bayan ya yi jawabi ga membobin Babban Kwas na 46 na Kwalejin Runduna da Ma’aikatan Sojoji (AFCSC) da ke Jaji a Kaduna ranar Talata.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa ministan, wanda ya kai ziyarar aiki, ya gabatar da jawabi ga mahalarta kwas ɗin a wani taron ƙara wa juna sani da kwalejin ta shirya kan yaƙi da ta’addanci.

Ministan ya zagaya sansanin Kabala da Selaya, inda ake harbi da bindiga, da sansanonin horaswa a cikin ƙaramar barikin soja ta Jaji.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?