Back

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga da dama a Zamfara, sun ceto mutane takwas 

Rundunar sojin hadin gwiwa ta Operation Hadarin Daji ta Arewa maso Yamma ta bayyana cewa, ta kashe ‘yan bindiga da dama tare da ceto wasu mutane takwas da aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara.

Jami’in yada labarai na Operation Hadarin Daji, Laftanar Kanar Suleiman Omale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Gusau.

Omale ya ce, “A ranar 28 ga watan Fabrairun 2024, sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’adda da suke dauke da muggan makamai wandanda saboda wuta da karfin bindigogin sojojin ya sa ‘yan ta’addan suka tsere cikin daji cikin rudani kuma suka yi watsi da wadanda suka kama su.

“Rundunar sojojin sun kashe ‘yan ta’adda da dama, sun lalata yankunan ‘yan ta’addan tare da mamaye yankin da yin sintiri mai karfi domin karfafawa mazauna shiyyar gwiwa.”

Ya ce an mika duk wadanda aka ceto ga hukumomin da suka dace domin su kasance cikin ni’imar dangin su.

Kwamandan rundunar, Manjo Janar Godwin Mutkut, wanda kuma shi ne babban kwamandan runduna ta 8 ta sojojin Najeriya, ya yabawa kokarin sojojin bisa ci gaba da jajircewa da suke yi a kokarin dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma. .

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin da suka fi fama da  ‘yan bindiga.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?