Dakarun runduna ta daya ta sojojin Najeriya a ranar Laraba sun yi nasarar kawar da wani kasurgumin dan bindiga da aka bayyana sunan shi da Boderi wanda ake zargin shi ya kitsa sace-sacen mutane da dama da suka hada da ‘yan matan makarantar Yauri, Jami’ar Greenfield da kuma harin makarantar horas da sojoji ta Najeriya.
An ce an kashe Boderi ne tare da wani sarki Bodejo a harin kwanton bauna.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar. Onyema Nwachukwu a cikin wata sanarwa a yau ne ya bayyana hakan.
Nwachukwu ya bayyana cewa an kai harin ne a wani harin kwanton bauna da aka kai a kan hanyar Bada zuwa Riyawa da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.
“A arangamar, sojojin sun kashe ‘yan ta’adda shida tare da kwato bindigogin AK 47 guda biyu, mujallun bindigu biyar AK 47, harsashi na musamman 7.62mm guda dari uku da kuma babura sha tara da aka lalata.”
A wani samame na daban da suka kai a kananan hukumomin Igabi, Giwa da Birnin Gwari na jihar Kaduna, sojojin runduna ta daya “sun kashe ‘yan ta’addan tare da kwato wasu bindigogi da alburusai a arangamar da suka yi da mahara.
Duk da haka, sojojin sun yi hasashen ci gaba da ayyukan da za a yi domin fatattakar ‘yan ta’adda daga wadannan yankuna da kuma taimaka jama’a.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar ya kara da cewa dakarun sojojin a lokacin da suke sintiri, sun yi artabu da ‘yan ta’adda a kan hanyar Maganda-Dausayi zuwa Mugaba.
Ya ce duk da cewa ba a iya tantance adadin maharan ba, amma sojojin sun kashe biyu daga cikin maharan tare da kwato bindiga kirar AK 47 guda daya, Mujallar AK 47 guda uku, kirar 7.62mm na musamman, wayar Techno 1, Hilux 3 da kuma makullan babura. Da kuma ganyayyyaki da ake zargin tabar wiwi ce, kwalayen tramadol da kuma Naira dubu goma sha uku kacal,” a cikin fafatawar da aka yi na kusan awa daya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A yayin da sojojin ke sintiri a kan titin Maganda zuwa Dausayi zuwa Mugaba, sojojin sun fuskanci luguden wuta daga ‘yan tada kayar baya da suka hada da barayin shanu yayin da suka bude wa sojojin wuta kai tsaye.
“’Yan ta’addan da ba a iya tantance adadin su ba, sun bude wa sojojin wuta daga jikin garken dabbobi wanda hakan ya sa sojojin suka mayar da martani nan take.”
“Abin takaici, wasu daga cikin dabobin da ‘yan fashin suka buya a bayan su, sun mutu sanadiyyar musayar wutar sa aka yi inda harsashi ya same su a lokacin arangamar. Har yanzu sojoji suna nan suna bin maharan da suka tsere kuma suna ci gaba da jajircewa wajen kawar da su daga yankin da ke da tashe tashen hankula.”
Nwachukwu ya bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa sojojin Najeriya hadin kai da sauran jami’an tsaro a yakin da ake yi da ta’addanci da tada da kayar baya a kasar.