Back

Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 212, sun kama wasu 252, inji Hedikwatar Tsaro

Hedikwatar Tsaro a ranar Alhamis ta ce sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 121, sun kama 253 tare da kuɓutar da mutane 244 da aka yi garkuwa da su a wasu ayyuka daban-daban a faɗin ƙasar cikin mako guda.

Daraktan Tsaro, Ayyuka na Yaɗa Labarai, Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayar da ƙarin haske kan ayyukan sojoji a ranar Alhamis a Abuja.

Buba ya ce sojojin sun kuma ƙwato makamai iri-iri 223 da alburusai 2,756 da suka haɗa da bindigogi ƙirar M56 guda uku, bindigogin AK47 guda 115, bindigar PKT uku, bindigu na gida guda 24, da kuma bindigunoni 36.

Ya ƙara da cewa sun ƙwato bindigogin gida guda bakwai, guda 1,716 na harsashe na musamman mai girman 7.62mm, 494 na 7.62mm na NATO, da kuma 60 na harsashe mai girman 7.62 x 25mm da dai sauransu.

A yankin Arewa maso Gabas, Buba ya ce dakarun Operation Haɗin Kai sun kashe ‘yan ta’adda 52, sun kame 137 tare da kuɓutar da mutane 78 da aka yi garkuwa da su a cikin wannan makon.

Ya ƙara da cewa sojojin sun kuma ƙwato bindigogin M56 guda uku, AK47 guda 40, bindigu na PKT guda uku, bindigu na ƙirƙira 13, gurnetin hannu guda biyu, 889 na harsashe na musamman mai girman 7.62mm da dai sauransu.

A yankin Arewa ta tsakiya, Mista Buba ya ce dakarun Operation Safe Haven da Whirl Stroke, sun kashe ‘yan ta’adda 47, sun kama 17 tare da kuɓutar da mutane huɗu da aka yi garkuwa da su, da ƙwato tarin makamai.

A yankin Arewa maso Yamma, kakakin rundunar tsaron ya ce dakarun Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan ta’adda 62, sun kame wasu 12 tare da kuɓutar da mutane 162 da aka yi garkuwa da su.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?