Back

Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 2,351, sun kama 2,308 a cikin watanni 3, inji Hedikwatar Tsaro

Hedikwatar Tsaro (DHQ) a ranar Alhamis ta ce sojojin da aka tura wurare daban-daban na ayyuka a faɗin ƙasar sun kashe ‘yan ta’adda 2,351 tare da kama mutane 2,308 a cikin kwata na farko na shekarar 2024.

Rundunar sojin ta kuma ce sojojin sun kuɓutar da mutane 1,241 da aka yi garkuwa da su.

Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro, Manjo- Janar Edward Buba, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, ya ce sojojin sun hana wasu da ake zargin ɓarayin mai ne ɗanyen mai da aka ƙiyasta kuɗinsa ya haura naira biliyan 20 (N20,331,713,910.00) kawai.

Ya ce daga cikin waɗanda aka kawar akwai manyan kwamandojin ‘yan ta’adda.

Ya ce an kashe su ne ta hanyar haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin sojojin sama da na ƙasa da sauran jami’an tsaro.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?