Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda aƙalla biyar a wani samame da suka kai a jihar Borno.
A ranar Juma’a ne aka ceto mutane 78 da aka yi garkuwa da su, waɗanda suka haɗa da mata 35 da yara 43.
Sojojin sun yi nasarar tsarkake ƙauyuka shida da ‘yan ta’addar ke gudanar da ayyukansu.
Ƙauyukan da aka share sun haɗa da Ngurusoye, Sabon Gari, Mairamri 1 da 2, Bula Dalo, Bula Dalo tsawo, Yamanci, da Gargaji duk a jihar Borno.
Wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojojin Nijeriya, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a ranar Asabar ya ce an samu nasarar ne bayan wani ƙazamin artabu da ‘yan ta’addan.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Dakarun runduna ta 7 ta sojojin Nijeriya sun ci gaba da kai farmaki kan mayaƙan ƙungiyar Da’ish ta yammacin Afrika da takwaransu na JAS a arewa maso gabashin Nijeriya.
“A wani mumunar sintiri da rundunar soji ta gudanar a ranar Juma’a, 22 ga watan Maris, 2024, da rundunar soji ta yi nasarar fatattakar wasu ƙauyuka shida da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su.
“A yayin samamen, rundunar ta ci karo da ‘yan ta’addan kuma suka yi mumunar fafatawa da ‘yan ta’addan, inda suka kawar da biyar daga cikin ‘yan ta’addan. Jajirtattun sojojin sun kuma ceto mutane 78 da suka haɗa da mata 35 da yara 43 da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su.
“Yankunan da ƙauyukan da CT din ta share sun haɗa da Ngurusoye, Sabon Gari, Mairamri 1 da 2, Bula Dalo, da Bula Dalo. Sauran yankunan kuma da aka share sun haɗa da Yamanci da Gargaji gaba ɗaya. Abubuwan da aka ƙwato sune tutar ‘yan ta’adda ɗaya da wayar hannu ta ‘yan ta’addar. Waɗanda aka ceto dai suna tsare ne domin gudanar da bincike na farko da kuma bayyana bayanansu.
“Sojojin sun ci gaba da gudanar da ayyukan Desert Sanity III na kawar da ‘yan ta’adda da masu tayar da ƙayar baya daga da Arewa maso Gabas daga.”