Back

Sojoji sun lalata haramtattun wuraren tace mai a Rivers

Rundunar sojojin Nijeriya ta musamman mai suna “Operation Delta Safe” ta kai harin bama-bamai a wasu haramtattun wuraren tace mai da wasu sansanonin masu yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa a Rivers a ranakun Juma’a da Asabar.

Daraktan Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Saman Nijeriya, AVM Edward Gabkwet, ya bayyana a ranar Lahadi a Abuja cewa hare-haren da jiragen suka kai na rage ƙarfin ɓarayin mai sosai.

Ya ba da tabbacin cewa hare-haren sun tabbatar da cewa masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa sun daina fasa magudanonin mai domin satar ɗanyen mai.

Gabkwet ya bayyana cewa an lalata wani haramtaccen wurin tace mai a unguwar Idama sannan an lalata wasu kwale-kwale guda huɗu waɗanda bincike ya gano na ɗauke da kayayyakin da aka tace ba bisa ƙa’ida ba.

“An gudanar da bincike makamancin haka a kan al’ummar Ogbomkiri inda aka gano wani haramtaccen wurin tace mai tare da lalata shi.

“Bincike kan al’ummar Arugbana ya nuna cewa ɓarayin mai na ƙoƙarin kafa wani haramtaccen wurin tace mai, kuma da suka ga jirgin da ke gabatowa, sai suka ranta a na kare.

“An kuma lura da wasu haramtattun wurare a unguwar Samkiri kuma an lalata su.

Gabkwet ya ƙara da cewa, “A gaba ɗaya, an gano haramtattun wuraren tace mai, da jiragen ruwa huɗu, tare da lalata su a cikin aikin na kwanaki biyu.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?