Back

Sojoji sun sallama wa matsi, sun saki editan da aka sace

Editan Jaridar FirstNews Online, Segun Olatunji, ya samu ‘yanci bayan ya shafe kwanaki 12 a tsare.

Wasu ‘yan bindiga sanye da kayan sojoji sun kai farmaki gidan Olatunji da ke Iyana Odo a yankin Abule Egba a jihar Legas a ranar 15 ga watan Maris inda suka yi awon gaba da shi.

Yayin da iyalan ɗan jaridar ba su samu wani saƙo daga waɗanda suka yi garkuwa da shi ba, mahukuntan kafar yaɗa labaran sun danganta lamarin da wani labari da FirstNews ta wallafa.

An ci gaba da nuna damuwa game da inda ya ke har zuwa lokacin da Cibiyar Yaɗa Labarai ta Ƙasa da Ƙasa (IPI Nigeria) ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa editan yana hannun Hukumar Leƙen Asiri ta Tsaro (DIA), wata hukuma da ke ƙarƙashin jagorancin Manjo Janar Emmanuel Undiandeye, wanda shi kuma yake bayar da rahoto ga Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Chris Musa.

Sa’o’i kaɗan bayan da IPI ta bayyana haka, Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya shaida wa wasu editoci cewa sojoji sun tabbatar da cewa editan na hannunsu.

A halin da ake ciki kuma, a wata sanarwa mai kakkausar murya a ranar Laraba, IPI ta yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi amfani da ikon ofishinsa a matsayinsa na Babban Kwamandan Sojojin Nijeriya ya umurci Babban Hafsan Tsaro (CDS) ya samar da Olatunji.

“IPI Nijeriya ta samu tambayoyi game da wannan batu daga ko’ina a duniya. Cibiyar ta kuma tuntuɓi Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, da Sojojin Nijeriya, da Hukumar Leƙen Asiri ta Tsaro, da Hedikwatar Tsaro, da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, inda suka buƙaci a sake shi. Duk ƙoƙarin da aka yi a wannan ɓangaren ya ci tura zuwa yanzu.”

“Hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan jarida da masu rajin kare haƙƙin bil’adama a duniya cewa sojojin Nijeriya na iya ɓoye wasu muhimman bayanai da suka shafi lafiyar ɗan jaridar daga jama’a.

“Don haka IPI tana kira ga Shugaban Ƙasa Tinubu da ya umarci hukumomin sojin iajeriya da su gaggauta sakin Mista Olatunji ko kuma a gurfanar da shi a kotu idan ya aikata wani laifi. Ya kuma kamata ƙasashen duniya su mai da hankali kan tsare Mista Olatunji na rashin adalci da sojojin Nijeriya suka yi,” a cewar sanarwar da shugaban IPI, Musikilu Mojeed, da Tobi Soniyi, sakataren ta suka sanya wa hannu.

A safiyar ranar Alhamis ne aka sako Olatunji ga Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE), a cewar wani saƙo daga sakataren ƙungiyar, Dakta Iyobosa Uwugiaren.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?