Back

Sojoji za su iya kawo ƙarshen matsalar tsaro, inji Kwankwaso

Rabi’u Musa Kwankwaso

 

Tsohon Ministan Tsaro, Sanata Musa Kwankwaso, ya ce sojoji za su iya kawo ƙarshen matsalar tsaron da ƙasar nan ke fuskanta a halin yanzu.

Kwankwaso, wanda kuma Shugaban jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) na ƙasa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron Kwamitin Zartarwa na NNPP a Abuja.

Ya ce duk da cewa haƙƙin Gwamnatin Tarayya ne ta magance matsalar tsaro, ‘yan Nijeriya ma na da muhimmiyar rawar da za su taka ta hanyar isar da muhimman bayanai ga hukumomin tsaro.

“A matsayina na tsohon Ministan Tsaro kuma tsohon Babban Jami’in Tsaro na Jihar Kano na tsawon shekaru takwas, wanda ya yi yawo kuma ya san wannan wasa na siyasa sosai, na yi imanin cewa tunkarar matsalar tsaro alhakin Gwamnatin Tarayya ne a yanzu.

“Mun ga jihohi suna kafa wasu rundunonin tsaro. Wani lokacin ka yi dariya. Matsayin da yake a yau yana kan matakin sojan Nijeriya ne kuma duk abin da ya yi ƙasa da hakan ba zai yi aiki ba.

“Kuma dole ne kowa ya haɗa kai don ganin an samu zaman lafiya a ƙasar nan.

“Wasu daga cikinmu da ke ƙauyuka da ma garuruwa muna iya tunawa da yadda mutanenmu suke zuwa gonaki. Yanzu mutane ba za su iya zuwa gona ba. Ana kuma fatattakar su daga ƙauyuka da garuruwansu.

Ya ce, “masu aikata laifuka da ‘yan bindiga suna cin zarafin yaranmu kullum tare da sace ɗaruruwan su,” inji shi.

Kwankwaso, wanda kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa na NNPP 2023 ne, ya ce jam’iyyarsa tana da tsarin da za ta bi don magance matsalolin da sauran ƙalubalen da ke addabar ƙasar idan ‘yan Nijeriya suka ba su dama.

Ya ce jam’iyyar NNPP ita ce kawai fata ga ‘yan Nijeriya, yana mai cewa jam’iyyun APC da PDP sun yi ƙasa a gwiwa.

Da yake jawabi, Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano, ya buƙaci ‘yan jam’iyyar da su kasance masu ƙwarin gwiwa wajen sadaukar da kai ga jam’iyyar, inda ya ce babu wani abu kamar kashi 99 cikin 100 na biyayya ga jam’iyyar, sai dai kashi 100 cikin 100.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?