Back

Sojojin Najeriya sun tarwatsa maboyar ‘yan bindiga, sun ceto mutane hudu da aka yi garkuwa da su a Taraba, 

Sojojin Najeriya, Bataliya ta 114 tare da hadin gwiwar jami’an tsaro, a ranar Asabar sun lalata maboyar ‘yan bindiga da dama tare da kubutar da wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Yorro ta jihar Taraba.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Laftanar Olabodunde Oni, mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 6, kuma aka rabawa manema labarai a Jalingo ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa an fara daukar matakin gaggawa na fatattakar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane wadanda ke kawo cikas ga zaman lafiya a Yorro da kewaye tun a ranar 2 ga Fabrairu na shekarar nan.

Sanarwar ta kuma yi nuni da cewa, sojojin sun yi arangama da ‘yan bindiga a tsaunin Gampu da Ban Yorro inda suka yi amfani da karfin wuta, lamarin da ya sa ‘yan bindigar suka tsere daga wurin, inda suka bar mutane hudu da suka sace.

“Har yanzu ana ci gaba da gudanar da aikin fatattakar ‘yan bindigar domin tabbatar da ganin an gano sauran wadanda aka yi garkuwa da su, da Kuma bin diddigin sauran ‘yan bindigan da suka tsere daga yankin a yayin musayar wuta domin sake haduwa da ‘yan uwansua wani wurin.

“Wadanda aka ceto sune, Genesis Samuel, mai shekaru 24, daga kauyen Ganku; Benard Denis, mai shekaru 28, daga kauyen Fulfualgon; Esther Titus, 35, daga kauyen Kosanai; da kuma dan Sarkin Pupulle, Isma’il Umar, mai shekaru 25, wanda aka yi garkuwa da shi daga gidan shi a ranar 18 ga watan Janairu.

Kamar yadda sanarwar take,  “Rundunar Brigade ta himmatu wajen tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan kasa da kuma wargaza duk wasu ababen da suka shafi aikata laifuka a jihar.”

Sanarwar ta kara da cewa, “An bukaci jama’a da su ci gaba da baiwa sojojin goyon baya ta hanyar ba da sahihan bayanai masu inganci domin taimakawa wajen inganta tsaro a cikin jihar baki daya.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?