Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Legas ta ce Rundunar Sojin Nijeriya ta miƙa ma ta wani soja da aka kora tare da wasu mutane uku bisa zarginsu da yin basaja a matsayin sojoji.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da miƙawar ga Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ranar Lahadi.
Hundeyin ya ce wani Kyaftin na Sojoji (wanda ba a ambaci sunansa ba), wanda ke Dodan Barrack, Obalende, ya kawo mutanen huɗu (waɗanda aka ɓoye sunansu), zuwa Sashen ‘Yan Sanda na Onikan ranar Juma’a da misalin ƙarfe 5.01 na yamma.
Ya ce duk waɗanda ake zargin ba su da takamaiman adireshi, ya ƙara da cewa an kori ɗaya daga cikinsu daga aikin Soja a shekarar 2016.
Hundeyin ya ce an kama waɗanda ake zargin sanye da kayan ɓadda kama, riga, da hula na sojojin Nijeriya.
“Da aka yi musu tambayoyi, an gano cewa waɗanda ake zargin suna yawan aikata laifuka daban-daban ta hanyar amfani da kayan aikin soja kuma suna amfani da su a wuraren binciken ababen hawa.”
Ana ci gaba da ƙoƙarin gano yadda suka samu kakin sojojin. Ana ci gaba da gudanar da bincike,” inji shi.