Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Nijeriya (SSANU) da Ƙungiyar Ma’aikatan Jami’o’i Da Ba Na Koyawar ba (NASU), sun ayyana yajin aikin gargaɗi na kwanaki 7, domin neman a biya su albashin ma’aikatan su na tsawon watanni huɗu, bayan yajin aikin 2022 a faɗin ƙasar.
Matakin na daga cikin ƙudurin kwamitin haɗin gwiwa na ƙungiyoyin biyu, bayan wani taro da suka gudanar a Akure a ƙarshen mako.
A cewar shugaban SSANU, Mohammed Ibrahim, wanda ya karanta wa manema labarai sanarwar taron a Abuja ranar Litinin, matakin fara yajin aikin gargaɗi a matsayin matakin ƙarshe ne tunda wasiƙun zanga-zanga da dama da wasu maganganu tare da Gwamnatin Tarayya bai haifar da biyan albashin da aka hana ba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Idan har Gwamnatin Tarayya ba ta yi wani abu ba don magance wannan lamarin da kuma amsa wasiƙun da muka rubuta musu a baya, zai iya zama tilas mambobin ƙungiyoyin biyu su yi taro nan ba da jimawa ba domin ɗaukar duk wani mataki da ya dace kan lamarin.
Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin biyan ma’aikatan jami’o’in da aka hana su albashi sakamakon yajin aikin da suka yi a shekarar 2022.
Sai dai SSANU, NASU, da kuma Ƙungiyar Malaman Fasaha ta Ƙasa (NAAT) sun ce har yanzu ba su samu albashi na wannan lokacin ba, kuma sun bayar da wa’adi mako guda kimanin makonni biyu da suka gabata.
Da yake magana a gidan Talabijin na Channels a shirin Sunday Politics, shugaban SSANU yayi zargin Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da ƙungiyoyin.
“Dole ne mu yi magana irin haka saboda an nuna mana a fili cewa ba mu da komai a cikin tsarin. Amma duk mun san cewa babu wata jami’a da za ta iya aiki ba tare da ma’aikatan da ba na koyarwa ba saboda yawancin mu ƙwararru ne. Mu ne muke da injin gudanarwar kowace jami’a. Suna mu’amala da wannan ɓangaren na ma’aikata da raini. Ba abu bane mai kyau game da tsarin,” inji shi yayin shirin.
“Duk da muna godiya ga Gwamnatin Tarayya da ta biya takwaranmu na ilimi, muna kuma ganin ya zama dole a biya mambobin mu suma,” inji sanarwar.