Back

Super Eagles sun yi sadaukarwa don farin cikin ‘yan Nijeriya, inji Peseiro

Koci Jose Peseiro yana ba Victor Osimhen umarnin dabara a Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka na 2023 (Afcon) a Cote d’ivoire

Tsohon kocin Super Eagles, José Peseiro, ya ce ‘yan wasan babbar tawagar maza ta ƙasa sun yi sadaukarwa don farin cikin ‘yan Nijeriya.

Da yake magana a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter), kocin ɗan ƙasar Portugal ya godewa ‘yan Nijeriya da kuma ‘yan jaridu bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake jagorantar ƙungiyar.

“Ina so in gode wa dukkan ‘yan Nijeriya da ɗaukacin ‘yan jaridu saboda sha’awa, goyon baya, da kuma ƙwarin gwiwa da suka baiwa Super Eagles lokacin da nake kocinsu. Ina so in nemi dukkan ku da ku ba wa ‘yan wasan ku goyon baya a koyaushe.

“Waɗannan ’yan wasan suna sadaukar da komai ga Super Eagles, suna alfahari da wakiltar ƙasarsu. ‘Yan wasan suna sadaukarwar don kawo muku farin ciki.”

Ya ƙara da cewa, “Super Eagles sun cancanci duk goyon bayan ku, wanda zai kasance mai muhimmanci ga manyan ƙalubalen da ke gaba.”

Kocin ɗan ƙasar Portugal wanda ya ajiye aikinsa a makon da ya gabata bayan ƙarewar kwantiraginsa da Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya, NFF, ya kuma nemi ‘yan Nijeriya da su ci gaba da marawa Super Eagles baya a kowane yanayi.

A tsawon watanni 22 da ya yi da zakarun nahiyar Afirka sau uku, ya jagoranci Super Eagles a wasanni 23. A ƙarƙashin jagorancin nasa, ƙungiyar ta samu nasara 11, asara 7, da canjaras 4.

Super Eagles dai ta samu nasara a wasanni huɗu sannan ta sha kashi a wasanni shida cikin 10 da ta buga a shekarar da ya fara zama kocinta.

Daga cikin shidan da aka yi rashin nasara, biyar har da wasannin sada zumunta.

An fara wasanni goman ne da wasansa na farko da Mexico a wasan sada zumunci a Texas a ranar 29 ga Mayu, 2022, inda Nijeriya ta doke Saliyo da ci 3-2 a ranar 18 ga watan Yunin 2023.

Super Eagles dai ta samu nasara sau bakwai, ta yi kunnen doki huɗu, ta kuma yi rashin nasara a wasanni biyu daga cikin sauran wasanni 13 da ta buga bayan an tsawaita kwantiraginsa a watan Satumban 2023.

Ƙungiyar ta samu nasara a wasanni biyar daga cikin bakwai a gasar AFCON ta 2023, inda ta yi canjaras a wasanta na farko da Equatorial Guinea, sannan ta yi rashin nasara a wasan ƙarshe da ƙasar, wanda hakan ya sa ta zama ta biyu a gasar.

Tsohon kocin Saudiyya da Venezuela ya jagoranci ƙungiyar zuwa matsayi na biyu a Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) ta 2023 kuma gwamnatin tarayya ta karrama ta da lambar yabo ta ƙasa da kadarorin ƙasa da kuma gida.

Kawo yanzu dai hukumar ta NFF ba ta bayyana sunan wanda zai maye gurbinsa ba amma an samu labarin sabon kwantiragin da ya kai dala 80,000 a wata wanda har yanzu bai karɓa ba.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?