Back

Tabarbarewar tattalin arziki: ‘Yan sandan Legas sun sha alwashin dakile masu zanga-zanga

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta sha alwashin dakile masu zanga-zanga da ke kokarin hana zirga-zirgar ababen hawa a Jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi.

A cewar shi, ‘yan sanda sun san shirin da wasu mutane ke yi na yin zanga-zanga a jihar kuma za su tabbatar da daukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Jihar Legas.

Ya jaddada cewa babu wani abu da zai hana zirga-zirgar ababen hawa cikin walwala ko kuma idan ana cikin yanayin zaman lafiya, saboda haka ya Nemi mazauna yankin da su gudanar da ayyukan su na halal.

“Wannan tabbacin ya zama wajibi ne biyo bayan rahotannin da aka samu game da zanga-zangar da za a fara a fadin kasar a ranar Litinin, ashirin da shida wannan watan, wanda hakan zai iya dakile ayyukan kasuwanci tare da dakile zirga-zirgar ababen hawa.

“Rundunar za ta yi aikin ta na tabbatar da cewa babu wani mutum ko gungun mutane da aka bari su keta haƙƙin ɗan adam, musamman ‘yancin walwala.

Don haka Adegoke ya gargadi duk masu niyyar yin zanga-zangar cewa duk wanda aka samu yana tauye hakkin wasu ‘yan Najeriya za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.

Adegoke ya kuma bukaci duk ‘yan Legas masu son zaman lafiya da su gudanar da ayyukan su na halal ba tare da fargabar tsangwama ko tsoratarwa ba, yana mai jaddada cewa an tura isassun kayan tsaro domin tabbatar da tsaron lafiyar al’umma.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?