Back

Tinubu ga gwamnoni da ‘yan Majalisar Dattawa: Mu haɗa kai don ganin Nijeriya ta zama babba

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira da a haɗa kai tsakanin gwamnatin tarayya, gwamnonin jihohi, da ‘yan majalisar tarayya domin cimma burin ci gaban ƙasa.

Shugaban Ƙasar ya yi wannan roƙo ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin gwamnoni da shugabannin Majalisar Dokokin Ƙasar a ranar Juma’a a Legas.

A ƙarƙashin jagorancin mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, tawagar ta haɗa da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio; Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara kuma shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya da sauransu.

Da yake magana a madadin Shugaban Ƙasa, Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya bayyana fatansa game da sake farfaɗo da tattalin arziƙin Nijeriya tare da yin kira da a haɗa ƙarfi da ƙarfe domin ciyar da ƙasa gaba.

Ya buƙaci haɗin kai a tsakanin duk masu ruwa da tsaki don samun ci gaba tare kuma ya yi alƙawarin samar da kyakkyawar makoma ga ƙasar nan a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Tinubu.

“ Mu haɗa kai domin kai al’ummar ƙasar tudun mun tsira. Zuwa Disamba, ina fata za mu sami dalilin yin murna,” inji shi.

Da yake jaddada matsayin Shugaban Ƙasa a matsayin jagoran haɗin kai wanda ya wuce ƙabilanci da addini, Shettima ya ce taron gwamnoni 27 da aka yi a Legas, tare da shugabannin Majalisar Dokoki da wasu tsofaffin gwamnoni, yana da nuna shaidar shugaba mara ƙabilanci wanda ya rungumi kowa.

“Wannan taro ya ratsa tsakanin ƙabilanci, addini da siyasa. Anan, muna da Fasto Eno na Akwa Ibom da Uba Hyacinth na Benue, kuma da Shugaban Ƙasa ya zauna, yana tambaya, ‘Ina Wammako, ina Yari’? Wannan shine alamar jagoranci na gaskiya. Abin da ya haɗa mu tare ya wuce duk abin da zai iya raba mu.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yaba wa gwamnonin Jihohin da suka yi koyi da salon jagorancin Shugaba Tinubu, na sauraron muryoyi daban-daban da tuntuɓar jama’a, ba tare da la’akari da siyasa ba.

“Gwamnonin suna aiki sosai. Zan iya cewa saboda na taɓa yin gwamna,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?