Back

Tinubu ga masu zuba jari na Ƙatar: Ku kawo min ƙarar duk wani jami’ina da ya nemi cin hanci

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a Ƙatar

Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ‘yan kasuwar duniya cewa Najeriya a shirye take ta gudanar da kasuwanci da gaske domin gwamnatinsa za ta yi maganin duk wata maslaha a ƙasar da ke kawo cikas ga masu saka hannun jari a tattalin arziƙin Najeriya, inda ya yi alƙawarin kawar da duk wasu guraben da ke kawo cikas ga harkokin kasuwanci.

A yayin da yake jawabi a wajen Taron Kasuwanci da Saka Hannun Jari na Najeriya da Ƙatar a birnin Doha, a ranar Lahadin da ta gabata, shugaba Tinubu ya shaidawa masu zuba jarin ƙasar Ƙatar cewa ana yin gyara da inganta babban tattalin arziƙin Afirka da tsarukan ta, ya kuma buƙaci shugabannin masana’antu na Ƙatar da su kai ƙarar duk wani jami’in gwamnati da ya nemi cin hanci a kowane lokaci a cikin harkokin kasuwancin su tare da cikakken tabbacin samun damar shiga ofishin Shugaban Ƙasa kai tsaye.

“Na zo nan ne domin in ba ku tabbacin cewa sauye-sauye na gudana; ku manta da duk abin da kuka ji a baya. Ko wani irin cikas ko matsala da wasunku za su iya fuskanta; a baya ne, domin babu cikas a nan gaba.

“Kada ku ba da cin hanci ga kowa daga cikin jama’armu, kuma idan an nema ko an karɓa daga gare ku, ku kawo mana ƙara. Za ku sami damar zuwa gare ni. Najeriya ba za a sake bayyana ta da abin da ya wuce ba, amma da abin da muke yi a yanzu da kuma zuwa gaba.

“Kada ku bari hasashe ya zama cikas ga nufin ku na saka hannun jari. Najeriya da gaske take game da kawo sauyi kan inganta zuba jari. Muna kawar da tarnaƙi a yau kuma za mu ci gaba da kawar da duk wani cikas.

“Mun yi abubuwa da yawa a cikin watanni tara. Kuma ina tabbatar muku da cewa kuɗaɗen ku za su shigo ƙasarmu kuma su fita salun alun. Ku kawo jarin ku,” in ji shugaban.

Bugu da ƙari, shugaban ya bayyana cewa yaƙi da cin hanci da rashawa da rashin tsaro a Najeriya ya ƙara ƙarfi sosai tare da naɗa tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Mallam Nuhu Ribadu, a matsayin Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA).

“Muna da mutumin da ya samu lambobin yabo da yawa a duniya kan yaƙi da cin hanci da rashawa a matsayin sarkin yaƙi da cin hanci da rashawa.

“Aikina shi ne in gaya muku cewa Najeriya a buɗe take don kasuwanci, kuma in tabbatar muku cewa jarin ku ba zai samu matsala ba a hannunmu. Muna da maza da mata masu suna mai kyau a nan. Kuma mun yi imanin za mu iya kafa kwamiti mai kyau wanda zai kai tattaunawarmu zuwa ga ƙarshe mai amfani.”

Shugaban ya kuma bayyana cewa Najeriya na da damammaki masu yawa a fannoni daban daban, inda ya shaida cewa: “Muna da mai da iskar gas; muna da ma’adanai masu tauri. Ban ga dalilin da ya sa ba za mu iya zama abokan hulɗa a cikin binciken ma’adinan ƙarfe, da samar da ƙarfe, da makamashi ba.

“Na zo nan ne don ba ku tabbaci a kowane fanni: yawon buɗe ido, saukar baƙi, kiwon lafiya, da sauran damammaki da yawa da ke kewaye da mu. Kada ku kasance masu saka hannun jari da suka rasa dama mai alfanu da muke bayarwa,” inji Shugaban.

Ministan Kasuwanci da Masana’antu na Ƙatar, Sheikh Mohammed bin Hamad bin Qassim Al Abdullah Al Thani, yayin da yake maraba da tawagar Najeriyar a gaban shugabannin masana’antu na ƙasar Ƙatar, ya ce ƙasarsa na fatan yin la’akari da damammaki a Najeriya, sakamakon yawan al’umma da kasuwarta, yayin da take neman ba da fifiko ga sabbin saka hannun jari a cikin shirye-shiryen ƙarancin fitar da iskar gas, samfuran ma’adinai, sinadarai na mai, masana’antu, da abubuwan amfani.

“Muna fatan yin aiki tare da takwarorinmu na Najeriya don cimma manufofinmu na haɗin gwiwa a waɗannan sassan,” inji Ministan.

Waɗanda suka raka Shugaban Ƙasar zuwa Taron Kasuwanci da Zuba Jari na Najeriya da Ƙatar sun haɗa da: Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum; Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani; Gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu; Ministan Tattalin Arziƙi da Ministan Kuɗi, Wale Edun; Ministan Ma’adanai, Dokta Dele Alake; Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate; Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arziƙin Ruwa, Mista Adegboyega Oyetola; Ministar Kasuwanci, Masana’antu da Zuba Jari, Dr. Doris Uzoka-Anite; Ministar Matasa, Dr. Jamila Bio Ibrahim; da Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur (Gas), Mista Ekperipe Ekpo.

Haka kuma a wajen taron akwai Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu; Mai Ba Da Shawara na Musamman kan Makamashi, Misis Olu Verheijen; da kuma Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa da Masana’antu, Ma’adinai da Noma ta Najeriya (NACCIMA), Mista Dele Kelvin Oye

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?