Back

Tinubu ya aika ƙudirin lamunin ɗalibai ga Majalisar Wakilai don nazari

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rubutawa Majalisar Wakilai wasiƙa yana neman a soke Dokar Lamunin Ɗalibai na 2023 da kuma kafa Dokar Lamunin Ɗalibai na 2024.

Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen, ya karanta wasiƙar da Shugaban Ƙasa ya bayar na janye lamunin ɗalibai a zaman majalisar na ranar Alhamis.

Shugaban Ƙasar a cikin wasikar ya bayyana cewa buƙatar soke Dokar Bayar da Lamuni na Ɗalibai na 2023 da kuma sake kafa sabuwar dokar ita ce ta magance wasu ƙalubale tattare da dokar da ta gabata da kuma inganta aiwatar da shirin ba da lamuni na ɗalibai da gwamnatinsa ta yi.

Wasiƙar ta ce, “Bisa ga Sashe na 58 (2) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, 1999 (wadda aka yi wa gyara). Ina gabatar da, Ƙudirin Lamunin Ɗalibai (Samar da Ilimi Mai Zurfi) (Sokewa da Sake Ƙaddamarwa), na shekarar 2024 don kyakkyawar la’akarin Majalisar Wakilai.

“Ƙudirin Lamunin Ɗalibai (Samar da Ilimi Mai Girma) (Sokewa da Sake Kaddamarwa), 2024 yana neman haɓaka aiwatar da Tsarin Lamuni na Manyan Makarantu ta hanyar magance matsalolin da suka shafi tsarin gudanarwa na Asusun Ba da Lamuni na Ilimi na Nijeriya (NELF), buƙatun cancantar masu nema, manufar lamuni, hanyoyin ba da kuɗi da hanyoyin biyan kuɗi.

“Duk da fatan wannan miƙatin za ta samu karɓuwa daga Majalisar Wakilai, don Allah a yarda, Mai Girma Shugaban Majalisa mai ritaya, da tabbacin mafi girman la’akarina.”

Ku tuna cewa a watan Yunin 2023, Tinubu ya rattaba hannu kan Ƙudirin kafa Asusun Lamuni na Ɗalibai wanda zai ba ‘yan Nijeriya lamuni marar riba domin samun ilimi mai zurfi.

A bara, Tinubu ya yi alƙawarin cewa shirin zai fara aiki daga watan Janairun 2024.

Duk da haka, ba a fara aiwatar da aikin ba, wanda hakan ya haifar da suka.

A ranar Larabar da ta gabata ne, Sakatare Janar na Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETFund), Sonny Echono, ya ce an samu tsaikon aiwatar da ƙudirin ne saboda wasu abubuwa da majilisar ta lura da su.

Masu ruwa da tsaki sun taɓo batutuwan da suka shafi tsarin Lamunin Ɗalibai, musamman ma da ya shafi buƙatun cancanta, hanyoyin samar da kuɗaɗe, hanyoyin bayar da kuɗaɗe da biyan kuɗaɗen da sauran su.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?