Back

Tinubu ya bada lambar yabo ta kasa MON ga yan wasan Super Eagles

Shugaba Bola Tinubu ya karrama ‘yan kungiyar wasan kwallon kafa ta kasa Super Eagles tare da bada lambar karramawa ta MON ga kowannen su da ya halarci gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka kammala.

A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana karbar bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles a zauren majalisar dokokin kasar.

Wannan taron na ranar Talata ya biyo bayan wasan da suka yi da kasar Cote d’Ivoire mai masaukin baki, a gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2023, inda suka dauki matsayin na biyu a cikin gasar.

A ci gaba da amincewa da nasarar da suka samu, gwamnatin tarayya ta hannun Ministan Babban Birnin Tarayya, Mista Nyesome Wike, ta bai wa kowane mamban tawagar fili a wani wuri da ba a bayyana ba.

Cikakkun bayanai daga baya…

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?