
Shugaban Ƙasa Tinubu
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi Allah wadai da satar ‘yan gudun hijira a jihar Borno da ɗalibai da malamai a jihar Kaduna.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Cif Ajuri Ngelale a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Juma’a, ya bayyana satar a matsayin mugun abu, ya kuma buƙaci jami’an tsaro da su gaggauta ceto waɗanda aka sace.
Shugaban ya ce bayan samun rahotanni daga jami’an tsaro kan al’amuran biyu, “Ina da yaƙinin za a ceto waɗanda abin ya shafa. Ni da iyalan waɗanda aka sace baza mu yarda da wani abu ba. Za a gudanar da adalci.
“Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da munanan abubuwan da suka faru na sace-sacen mutane masu rauni, da ‘yan gudun hijira a jihar Borno, da ɗalibai a jihar Kaduna.
“Shugaban Ƙasa ya umurci hukumomin tsaro da na leƙen asiri da su gaggauta kuɓutar da waɗanda abin ya shafa tare da tabbatar da cewa an yi adalci a kan waɗanda suka aikata waɗannan munanan ayyuka.
“Na samu bayanai daga shugabannin jami’an tsaro kan al’amuran biyu, kuma ina da yaƙinin za a ceto waɗanda abin ya shafa. Ni da iyalan waɗanda aka sace baza mu yarda da wani abu ba. Za a gudanar da shari’a sosai,” inji shi a lokacin da yake jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa, yana mai ba su tabbacin cewa nan ba da daɗewa ba za a haɗa su da ‘yan uwansu.