Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin cewa gwamnatin tarayya ta samar da tallafin abinci domin magance matsalar ƙarancin abinci a ƙasar.
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kan Jama’a ne Muhammed Idris ya bayyana haka a fadar shugaban ƙasa bayan taron Kwamitin Shugaban Ƙasa Kan Bada Agajin Gaggawa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Femi Gbajabiamila ya kira.
Idris ya ce gwamnati ta damu da halin da ‘yan Najeriya ke ciki kuma tana ɗaukar wasu matakai don ganin sun samu sauƙi.
Taron na ranar Talata na zuwa ne a daidai lokacin da ake gudanar da zanga-zanga a wasu sassan ƙasar Najeriya kan tsadar abinci da kuma tsadar rayuwa. Zanga-zangar dai ta ɓarke ne a jihohin Neja da Kano, lamarin da ya sa ake kira da a ɗauki matakin gaggawa na kawo karshen hauhawar farashin kayan masarufi.
Taron ya samu halartar Ministan Noma, Abubakar Kyari, Ƙaramin Ministan Noma, Mustapha Shehuri, Ministan Kasafi Da Tsare-tsare, Atiku Bagudu, Mai Bawa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Yemi Cardoso da dai sauransu.