Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya dawo Nijeriya bayan tafiyarsa ƙasashen Netherlands da Saudiyya.
A cewar NTA, Tinubu ya dawo ne ranar Laraba.
Blueprint ta ruwaito cewa Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, a cikin wata sanarwa ta kafar X ranar Talata, ya ce Shugaban Ƙasar zai dawo ranar Laraba.
“Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, tare da mataimakansa, za su dawo Nijeriya gobe daga Turai,” inji Onanuga.
Ku tuna cewa Tinubu ya bar Abuja ne ranar 22 ga Afrilu zuwa ƙasar Netherlands don wata ziyarar aiki.