Back

Tinubu ya jajanta wa iyalan waɗanda aka ƙona a masallacin Kano

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Jihar Kano dangane da gobarar da ta yi sanadiyyar mutuwar wasu masallata a wani masallaci da ke Larabar Abasawa a ƙaramar hukumar Gezawa a jihar.

Ajuri Ngelale, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Wayar da Kai a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata ya yi Allah wadai da wannan aika-aika tare da addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka samu raunuka a lamarin.

Daily Trust ta ruwaito cewa rikicin iyali kan rabon gado ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a unguwar Larabar-Albasawa da ke wajen Gezawa, hedikwatar ƙaramar hukumar Gezawa ta Jihar Kano.

An ce Shafiu Abubakar ya banka wa wani masallaci wuta a lokacin da masu ibada ke gudanar da Sallar Asuba da misalin ƙarfe 5:30 na safe.

An ce wanda ake zargin ya watsa wa masallacin man fetur, ya kulle ƙofar sannan ya banka masa wuta da masu ibada kusan 40 a ciki.

Shugaba Tinubu ya yi Allah-wadai da wannan aika-aikan da ya haifar da wannan mummunan lamari, ya kuma umurci jami’an tsaro da su yi bincike da hukunta waɗanda ake tuhuma.

Sanarwar ta ƙara da cewa “Shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasu, da duk waɗanda abin ya shafa, kuma ya yi addu’ar samun sauƙi cikin gaggawa ga waɗanda suka samu raunuka.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?