A ranar Laraba ne Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya bayar da lambar yabo ta ƙasa ga wasu sojoji 17 da aka kashe a yankin Okuama na jihar Delta.
A wajen jana’izar jami’an da sojoji da aka yi a Maƙabartar Sojoji da ke Abuja, shugaban ya kuma bayyana bayar da tallafin karatu da na gida ga yara da iyalan sojojin da aka kashe.
An kashe jami’an da sojojin ne a ranar 14 ga Maris, 2024 a lokacin da suka amsa kiran gaggawa bayan rikicin ƙabilanci tsakanin al’ummar Okuoma da Okoloba duk a Delta.
An karrama jami’ai huɗu da aka kashe da lambar yabo ta Members of the Order of Niger (MON) yayin da sojoji 13 da aka kashe aka karrama da lambar yabo ta Officers of the Federal Republic (OFR).
“Kowanne daga cikin mazan yanzu yana cikin jerin sunayen ma’aikata maza da mata waɗanda suka kare ƙasarmu tare da kare ‘yan uwansu ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da haɗarin da ke tattare da rayuwarsu ba.
“Dukkan su an ba su lambar yabo ta ƙasa a yanzu. An baiwa jami’ai huɗu kyautar lambar yabo ta Members of the Order of Niger (MON). Jajirtattun sojoji 13 da su ma suka rasa rayukansu, an ba su lambobin yabo na Officers of the Federal Republic (OFR),” inji Tinubu.
Tinubu ya ce za a riƙa tunawa da jiga-jigan sojojin a matsayin ’yan kishin ƙasa waɗanda suka amsa kiran aiki kuma suka rasa rayukan su.
“Yanzu ya zama wajibi mu kare iyalan jaruman mu da suka rasu. Gwamnatin Tarayya za ta samar da gidaje a kowane yanki na ƙasarmu ga kowane iyalan jami’an huɗu da sojoji 13 da ke cikinsu.
“Gwamnatin Tarayya ta kuma amince da bayar da tallafin karatu ga duk ‘ya’yan mamacin har zuwa jami’a har da waɗanda ke cikin mahaifa. Sojoji muna roƙon ku a cikin kwanaki 90 masu zuwa da ku tabbatar da cewa an biya dukkan kuɗaɗen mamatan.” inji Shugaban.