Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da naɗin ACM Shehu Mohammed a matsayin Shugaban Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC).
Naɗin na ƙunshe ne a wata takarda da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), George Akume ya fitar mai kwanan wata 20 ga Mayu, 2024.
Wasiƙar ta ce naɗin ya kasance daidai da sashe na 7 (1) na Dokar Kafa Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Tarayya, 2007 kuma zai fara aiki daga ranar 20 ga Mayu, 2024.
Shehu Mohammed ya karɓi muƙamin ne daga Dauda Ali Biu a matsayin Shugaban FRSC.