Back

Tinubu ya naɗa Yayale, Yuguda, Jega, da sauran su cikin Majalisar Shugabannin jami’o’i

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Alhaji Yayale Ahmed, da tsohon Gwamnan Bauchi, Alhaji Isa Yuguda, da tsohon Shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega, da sauran su a cikin jerin sunayen Majalisar Shugabannin jami’o’in tarayya da aka fitar.

Sauran waɗanda suka shiga jerin sunayen sun haɗa da Alhaji Muhammad Abacha, ɗan marigayi shugaban ƙasa Sani Abacha; Sanata Udoma Udo Udoma; Farfesa Munzali Jibril; Cif Wole Olanipekun SAN; Sen Joy Emordi da Farfesa Julius Okojie, da sauransu.

Jerin ya ƙunshi sunaye biyar kowannen su na jami’o’i 50, kwalejin kimiyya da fasaha 37 da kwalejojin ilimi 24.

Mutanen da aka zaɓa za su yi aiki a matsayin shugabannin jami’o’i da membobin Majalisar Gudanarwa ta jami’o’in tarayya 111, polytechnics da kwalejojin ilimi.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata talla da Ma’aikatar Ilimi ta fitar a ɗaya daga cikin jaridun ƙasar mai ɗauke da sa hannun Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Misis Didi Esther Walson-Jack.

Kamar yadda tallar ta ce, “Za a gudanar da taron ƙaddamar da Majalisar Shugabannin a ranakun Alhamis 30 ga watan Mayu da Juma’a 31 ga Mayu, 2024, a Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa, mai lamba 26 Aguiyi Ironsi Street, Maitama, Abuja. Duk taron biyu za su fara ne da ƙarfe 9 na safe kowace rana.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?