Back

Tinubu Ya Nada Sabbin Shugabannin Gudanarwa Na Kamfanin Wutar Lantarki Na Gwamnatin Tarayya 

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada shugabannin kamfanin samar da wutar lantarki na gwamnatin tarayya. Babban mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kai, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a yau Juma’a.

Bisa la’akari da muhimmiyar rawar da samar da wutar lantarki ke takawa wajen aikin masana’antu da bunkasuwar su, da kuma wani bangare na kokarin da ake yi na sake fasalin fannin wutar lantarki da tabbatar da tsaron makamashi ga daukacin ‘yan Najeriya, shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin mambobin tawagar gudanarwa.

Shugaba Tinubu ya yi hasashen cewa tare da cikakken kundin tsarin mulkin shugabannin gudanarwa, Kamfanin Wutar Lantarkin na gwamnatin tarayyar zai yi aiki tukuru domin ganin an cimma manufofin shirin Shugaban Kasa (PPI).

Ngelale ya bayyana cewa, an sake nada Kenny Anuwe a matsayin Manajan Darakta Kuma Babban Jami’in Gudanarwa (CEO), Sakataren Kamfanin wanda kuma shine mai ba da shawara kan harkokin shari’a, Mamman Lawan, shi ma an sake nada shi.

Sauran sun hada da Ebenezer Fapohunda da aka nada a matsayin babban jami’in fasaha na FIRS (CTO), Babatunde Oniru shi ne babban jami’in kasuwanci (CCO) yayin da Julius Olabiyi aka nada a matsayin babban jami’in kudi (CFO).

Shugaba Tinubu, a cewar Ngelale yana sa ran cewa tare da cikakken tsarin mulkin kwamitin gudanarwar, FGN Power Company Limited za ta yi aiki tukuru domin ganin an cimma manufofin shirin shugaban kasa na samar da wutar lantarki (PPI) tare da hadin gwiwa da Siemens Energy ta hanyar cikakken gyara.na zamani da kuma fadada hanyar sadarwa ta kasa da sauran muhimman matakai don tabbatar da ci gaban masana’antar samar da wutar lantarki ta Najeriya (NESI).

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?