Back

Tinubu ya rattaba hannu kan ƙudirin gyara lamunin ɗalibai don ya zama doka

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan ƙudirin gyara lamunin ɗalibai don ya zama doka, yayin da ya miƙa godiyarsa ga ‘yan Majalisar Dokokin Ƙasar kan yadda suka gaggauta tafiyar da ƙudirin.

Da yake jawabi bayan sanya hannu kan ƙudirin dokar a Fadar Shugaban Ƙasa, shugaban ya ce gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar ganin an baiwa ilimi kulawar da ya kamata ciki har da shirye-shiryen bunƙasa sana’o’i.

Ya ce, “Ɗazun nan na sanya hannu kan ƙudirin da ya ayyana lamunin ɗalibai yadda ya kamata. Da farko, dole ne in gode wa ’yan Majalisar Dokoki bisa gaggawar da suka yi wajen tafiyar da wannan kuɗiri bisa la’akari da ‘ya’yan Nijeriya, cewa ilimi shi ne makamin yaƙi da talauci yadda ya kamata.

“Mun ƙuduri aniyar tabbatar da cewa an baiwa ilimi kulawar da ta dace ga ƙasar nan gami da shirye-shiryen bunƙasa sana’o’i.

“Wannan shi ne don tabbatar da cewa babu wani, komai talaucin asalinsa, da aka cire shi daga samun ingantaccen ilimi da damar gina makomarsa.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?