Back

Tinubu Ya Tabbatar wa da ASUU Nagartaccen Jin dadin rayuwa domin gujewa yajin aiki 

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ’yan kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) cewa za’a kula da jin dadin su yadda ya kamata domin hana su yawaita yajin aiki don samun biyan bukatun su.

Shugaban wanda ya samu wakilcin daraktan ilimi na jami’ar ma’aikatar ilimi ta tarayya, Ochodo James, a wajen taron hadin gwiwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ta Bauchi (ATBU) jiya a Bauchi ya ce gwamnati za ta magance musabbabin yajin aikin da ke haddasa barnar da ba za a iya maye gurbin ya ba. 

Tinubu yace, ya tabbatar da juriyar malaman gaba da firamare, musamman wadanda ke bangaren jami’a. “Kun yi kyawawan ayyuka na tsawon lokaci duk da mawuyacin yanayi da ake ciki.

“Za mu yi duk abin da za mu iya yi iyaka bakin kokarin mu domin tabbatar da cewa jami’a a Najeriya ta sami ci gaba ta hanyar inganci yadda zai zamo dai-dai da tsarin takwarorin su na duniya.”

“Jami’o’in Najeriya sun shiga wahalhalun da ba a taba gani ba na tsawon shekaru saboda yajin aikin da ake yi. Yanzu mun mai da hankali kan samar da tsari mai dacewa don tattaunawa mai dorewa.”

“Za mu kawo karshen yajin aikin da kungiyoyin ma’aikata ke yi akai-akai na dindindin. Za mu magance wasu abubuwan da ke haifar da yajin aiki a jami’o’in mu da sauran manyan makarantun mu,” inji shi.

Shugaba Tinubu ya yi Allah-wadai da halayen wasu ‘yan Najeriya da ke zuwa jami’o’in da ke kasashen waje domin samun digiri na bogi.

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed wanda ya samu wakilcin mataimakin shi Auwal Jatau ya yabawa gudunmawar da jami’ar ke bayarwa wajen bunkasa ilimi a kasar nan.

Mataimakin shugaban jami’ar ATBU, Farfesa Muhammad Abdul’aziz ya yabawa gwamnatin tarayya bisa goyon bayan da take baiwa tallafin karatu na jami’o’i a kasar nan

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?