Back

Tinubu ya taya shugaban UBA, Elumelu murnar cika shekaru 61

Shugaban UBA, Tony Elumelu

A ranar Juma’a ne Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya taya Shugaban United Bank for Africa (UBA), Mista Tony Elumelu, murnar cika shekaru 61 a duniya.

Saƙon taya murnan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Mai baiwa Tinubu Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Ajuri Ngelale.

Sanarwar mai taken, ‘Shugaba Tinubu na taya babban jagoran ‘yan kasuwa, Tony Elumelu, murnar zagayowar ranar haihuwarsa.ʼ

“Shugaba Tinubu na yiwa Mista Elumelu fatan ƙarin shekaru masu yawa cikin ƙoshin lafiya da ƙarfin gwiwa yayin da yake ci gaba da ƙoƙarinsa na bayar da gudunmawa sosai ga ci gaban ƙasa da nahiyoyi,” inji sanarwar.

Tinubu ya yabawa babban ɗan kasuwan kuma mai taimakon jama’a, wanda ke shugabantar Heirs Holdings, Transcorp, United Bank for Africa, kuma shine ya kafa Gidauniyar Tony Elumelu.

Da yake yabawa Elumelu kan ƙoƙarinsa da kuma ƙwarewar sa wacce ke tafiyar da dukkan harkokin kasuwancinsa, shugaban ya amince da “irin hazaƙar da shugaban ‘yan kasuwar ke da shi wajen samar da jari da samar da damammaki ga matasan Afirka masu kuzari, da kuma ba su tallafin da suke buƙata don bunƙasa.”

Ya kuma godewa Elumelu, wanda a shekarar 2020 aka saka shi cikin jerin Mujallar Times na mutane 100 mafi tasiri a duniya, saboda tsayin daka da imaninsa ga Nijeriya da kuma yadda a kodayaushe yake nuna mafi kyawun al’ummar ƙasar.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?