Back

Tinubu ya umarci Hukumar Kwastam da ta mayar da kayan abincin da aka ƙwace ga masu su

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu

Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam (CGC), Bashir Adewale Adeniyi, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya umurci Hukumar Kwastam ta Nijeriya da ta mayar da dukkan hatsin da aka ƙwace ga masu su domin ci gaba da sayarwa a kasuwannin Nijeriya.

Kwanturolan ya bayyana hakan ne a yayin wani taron masu ruwa da tsaki a garin Kwangwalam da ke kan iyaka a ƙaramar hukumar Maiadua ta jihar Katsina ranar Asabar.

Ya ce shugaban ya bayar da wannan umarni ne a cikin gagarumin karimcinsa na tabbatar da cewa al’ummar ƙasar nan sun samu isasshen abincin da za su saya a farashi mai rahusa a kasuwanni.

Ya ce, duk da haka, mayar da kayan abincin da aka ƙwace ga masu su ya dogara ne kawai da sharaɗin cewa za a sayar da su a kasuwannin Nijeriya.

“Manufar shi ne a inganta samar da abinci da kuma tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya ba za su yi rayuwa da yunwa ba kuma Shugaban Ƙasa ya ɗauki wannan matakin a matsayin ɗaya daga cikin dabarun da za su taimaka wajen magance matsalar ƙarancin abinci.

“Muna da motoci sama da 120 na kayan abinci waɗanda za a kai ƙasashen waje da aka kama, wanda hakan ke nufin an fitar da kayan abinci da yawa daga kasuwanninmu, abin da ya kai ga rashin samuwa wanda ya haifar da matsin lamba kan farashin waɗannan kayayyakin.

“Don haka, muna fatan a lokacin da muka dawo da kayan kasuwanninmu, zai yi tasiri mai kyau kan farashin,” inji shi.

Kwanturolan ya ziyarci tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a mahaifarsa ta Daura da kuma Sarkin Daura, Dr Umar Farouq Umar a fadarsa inda sarkin ya ba shi sarautar gargajiya ta Mabuɗin Hausa.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?